Jihar Kano Zata bi Sahun Manyan Biranen Duniya

Jirgin zamani.

Za'a kawata sufiri a birnin Kano

Jihar Kano zata bi sahun manyan biranen duniya wajen samar da sufiri na zamani. Don kuwa gwamnatin jihar ta sa hannu a wata takardar yarjejeniya ta samar da layin jirgin kasa mai aiki da wutar lantarki da zai yi jigila a cikin birnin Kano.

Darektan kula da samar da sufiri na zamani a jihar kano Alhaji Najib Mahmud Abdusallal ya bayyana cewa, “wani kamfani dake birnin Bangkok ta kasar Thailand da hadin gwiwar wani kamfani dan kasa mai suna “Trust Railway” za su samar da jirgin sufiri a Kano.

Alhaji Najib Mahmud Abdullasalm ya kara da cewa, wannan aikin samar da layin jirgin kasa na zamani zai sha banban da sauran aiki domin kuwa ‘yan kasuwa ne zalla za su sa hannun jarinsu. Don haka aikin ba zai sami wani tsaiko ba”.

Kamar yadda zaku ji a rahoton Mohammed Salisu Rabi’u wakilin muryar Amurka a Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Kano Zata bi Sahun Manyan Biranen Duniya - 2'34"