Jihohin Arewa Ta Tsakiyar Najeriya Za Su Kafa Rundunar Tsaro - Gwamna Abdullahi

Injiniya Abdullahu Sule Gwamnan jihar Nasarawa

Jihohi shida da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya, sun yi matsayar kafa rundunar tsaro ta bai daya, a dai-dai sa'adda suke ganin sha'anin tsaro na kara tabarbarewa a kasar.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya shaidawa Muryara Amurka cewa an cimma wannan matsayar ne a wani taro da gwamnonin jihohin shida na Arewa ta tsakiya, su ka gudanar a jihar Nasarawa.

Gwamnonin sun yi matsayar samar da rundunar tsaro ta “Community Police” wadda gwamnatocin jihohin ne za su dauki nauyin tafiyar da ayukanta.

Injiniya Abdullahi Sule ya kara da cewa “Ko a ‘yan kwanakin nan sai da muka rantsar da ‘yan sa kai, domin taimakawa wajen samar da tsaro a jihar Nassarawa.”

Ya ce ana kuma ci gaba da tuntubar Sarakunan gargajiya lokaci zuwa lokaci, domin ganin an sanar da hukumomi a kan duk wasu bakin fuskoki da aka gani a cikin al’umma.

To sai dai ya ce suna aiki da jami’an tsaro na gwamnatin tarayya wajen ganin an hukunta duk wadanda aka samu da ayyukan ta’addanci.

Ga cikakkiyar zantawar da Yusuf Aliyu Harande ya yi da gwamnan jihar Nassarawa.

Your browser doesn’t support HTML5

"Zamu Samar Da Rundunar Tsaro Mallakar Jihohinmu" 3'10"