Jimillar Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Najeriya Ta Doshi 40,000

Jami'an Gwaijn COVID-19

Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum 591 da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma’a 24 ga watan Yuli.

A sanarwar da ta fidda a shafinta Twitter a daren ranar Juma’a, hukumar ta ce jihar Oyo ta samu karin mutum 191 yayin da jihar Lagos da ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar ta samu mutum 168.

Sauran jihohin sun hada da birnin tarayya Abuja inda aka samu mutum 61, sai Ondo 29, 26 a Osun, 24 a Ebonyi, 23 a Edo, 14 a Ogun, 13 a Rivers, 12 a Akwa Ibom, 10 a Kaduna, 6 a Katsina, 4 a Borno. Jihohin Delta, Ekiti da Imo kuma mutum 3 kowannensu, sai kuma 1 a Niger.

Gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yanzu ya kai 39,539, an kuma sallami mutum 16,559 bayan haka mutum 845 suka mutu.