Mataimakin shugaban kasar Kwesi Amissah-Arthur ne ya wakilci shugaba John Dramani Mahama a wurin kaddamar da tashin jirgin alhazan na farko
WASHINGTON, DC —
Da misalin karfe biyar na safiyar talatar nan agogon kasar Ghana, rukunin alhazan farko ya tashi zuwa kasar Saudiyya a gaban mataimakin shugaban kasar ta Ghana Kwesi Amissah-Arthur. Shugaban hukumar alhazan kasar Ghana alhaji Tanko ya tabbatarwa wakilin Sashen Hausa a birnin Accra, Baba Yakubu Makeri cewa sun kammala shirye-shirye tsaf a Ghana da kuma can kasar Saudiyyar, har wa yau ya ce sun dauki matakan kare lafiyar Mahajjatan kasar game da wani ciwon da hukumomin kasar ta Saudiyya suka ce ya bulla. Ga Baba Yakubu Makeri da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5