Jirgin Da Ya Dauki Gawar Tsohon Shugaban Kasar Amurka Daga Washington, Ya Isa Birnin Houston.

Jama'a da dangin George Hubert Walker Bush, za su yi ban-kwana na karshe da Shugaban Amurka na 41, a wata jana’iza da za a yi a garin Houston da ke jihar Texas.

A yau Alhamis, dangin George Hubert Walker Bush, za su yi ban-kwana na karshe da Shugaban Amurka na 41, a wata jana’iza da za a yi a garin Houston da ke jihar Texas.

Jirgin da ya dauki gawar tsohon shugaban daga Washington ya isa birnin Houston da yammacin jiya Laraba.

An kuma ajiye gawarsa a Cocin St. Martin Episcopal, inda zai kwana, domin a ba jama’a damar kallon akwatin da ke dauke da gawarsa, wanda aka rufe shi da tutar Amurka.

Bayan jana’izar sa, wacce mutane kalila ne za su halarta, za a dauki gawar a wani jirgin kasa na musamman, inda za a yi tafiyar kilomita 120 da ita zuwa inda za a binne shi, a Dakin Karatunsa da ke ginin Jami’ar Texas ta A&M.