Jihohin Najeriya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya

  • VOA Hausa

Wani yana kirga kudaden Najeriya

Jihohin Najeriya da dama sun kasa biyan albashin ma'aikata a dalilin karancin kudade da suke fuskanta.

Faduwar farashin mai ya haddasa kariyar tattalin arzikin Najeriya a dalilin dogaro da ta yi kan man fetur wajen samun kudin shiga domin biyan bukatunta.

Saboda haka wannnan nazarin da mujallar Economic Confidential ta yi bai zama abin mamaki ba ganin yadda Juhohi da dama suka dogara da kudin man fetur daga asusun Tarayya.

Masanin a fannin tattalin arziki, Abubakar Ali, ya jawo hankalin juhohi kan muhimmancin samar da kudin da za su samu na cikin gida.

Abubuwa da dama sun kara gurgunta tattalin arzikin Arewa maso yammacin Najeriya daga ciki har da fashi da makami da barayin shanu, inji Sanata Sa'idu dan Sadau.

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai ya kara da cewa har da mutuwar zuciyar mutane ta yadda ba sa rungumar sana'a wadda za ta iya tallafawa kudin shiga a jihohin.

Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El Hkaya domin jin cikakken bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Juhohin Najeriya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya "2'59