Juventus Ta Raba Gari Da Sarri

  • Murtala Sanyinna

Maurizio Sarri

Zakarun kasar Italiya wato kungiyar Juventus ta sallami mai horar da ‘yan wasan kungiyar Maurizio Sarri, shekara daya da soma aikinsa.

Sarri mai shekaru 61 ya koma kungiyar ne bara akan kwantaragin shekaru 3, bayan zaman shekara daya yana horar da ‘yan wasan Chelsea ta Ingila.

Duk da yake Sarri ya jagoranci Juventus din ta lashe gasar Serie A karo na 9 a jere, to amma kungiyar ta fusata ne daga ficewar da ta yi daga gasar zakarun Turai a ranar Juma’a, a wasan matakin ‘yan 16 na gasar da Lyon.

Juventus din ce ta yi galaba a wasan da ci 2-1, to amma ta yi waje-road ne saboda jumlar ci 2-2 a wasanni biyu na matakin, inda Lyon ta sami hayewa sakamakon kwallon da ta zura a wajen gidanta, sa’adda ta doke Juventus din da ci 1-0 a wasansu na farko.

Maurizio Sarri

Haka kuma kungiyar ta sha kashi a wasanninta 3 daga cikin 4 na karshe na gasar lig, inda maki daya ne kacal ya bambance tsakaninta da Inter Milan da ke dafa mata baya a teburin gasar.

Yanzu haka an soma baza rahotannin sunayen wadanda ake hasashen za su gaji Sarri a kungiyar ta Juventus, da suka hada da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino, da kocin Lazio Simone Inzaghi, da na Real Madrid Zinedine Zidane.