Kaduna: Gwamnati Zata sake Tantance Ma’aikata

Nasir El-Rufai Kaduna State Governor

Duk da kwarmaton da ma’aikata suka rika yi kafin gwamnati ta biyasu albashin watan da ya gabata, gwamnan jihar Kaduna Nasiru el-Rufa’I yace wannan watan ma sai an tantance ma’aikata kafin a biyasu albashin nasu.

Da yake jawabi a wani taron jin ra’ayoyin al’umma na shiya da aka shirya a garin Zari’a, ya bayyana irin makudan kudin da aka gano ana rubda ciki da su a gwamnatin jihar kowanne wata.

Da yake jawabi a wani taron jin ra’ayoyin al’umma na shiya da aka shirya a

Da yake jawabi a wani taron jin ra’ayoyin al’umma na shiya da aka shirya a garin Zari’a, ya bayyana irin makudan kudin da aka gano ana rubda ciki da su a gwamnatin jihar kowanne wata.

Mallam El-Rufa’I yace a bincike na farko da suka gudanar, sun dakile sace naira miliyan dari da ishirin a wannan watan, sai dai yace har yanzu ba a gama ba, domin bisa ga cewarsa, sun sani bisa ga bayanan da jama’a suke basu cewa, har yanzu akwai sauran kafofin da ba a toshe ba.

Ya bayyana cewa, akwai ma’aikatan boge har yanzu a ma’aikatu da dama, da kuma wadanda suka mutu amma har yanzu ana biyan albashi da sunansu. Banda haka kuma yace akwai likitocin da aka sani suna aiki a Abuja amma suna karbar albashi a Kaduna.

Gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa, a wannan karon, za a girke ‘yan sanda a wuraren da ake tantance ma’aikata wadanda za a bukaci su nuna takardunsu na daukar aiki kafin a biyasu albashi, idan aka tantance ma’aikacin boge ne, nan take za a saka amshi ankwa a tafi dashi.

Game da bayanin bada wa’adi a kan wadansu gidaje da aka ce an gina a filayen wadansu makarantu a birnin Zazzau, Mallam Nasiru el-Rufa’I yace ba gudu ba jada baya, ranar Laraba gwamnati zata fara ruguje gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Isa Lawal Ikara ya aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Kaduna-4:44"


.