Kalubalen Da Ke Gaban Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya yana rantsuwar kama aiki a wa'adi na biyu a yau 29 ga watan Mayu, 2019 (Saleh Shehu Ashaka)

Yayin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya shiga wa’adin mulki na biyu, ‘yan Najeriya, musamman masana da dama sun yi ta bayyana ra’ayoyi mabanbanta.

Buhari mai shekaru 76, ya shiga wannan wa’adi ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tsaro, musamman kan abin da ya shafi hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa, da kuma satar mutane da ake yi domin neman kudin fansa.

Hare-haren sun fi kamari ne a yankunan arewa maso yammacin kasar, kamar irinsu Zamfara, Katsina da sauran yankuna.

Tsaro Da Cin Hanci Da Rashawa

Idan aka yi waiwaye, a baya, da hawansa mulki a karon farko a shekarar 2015, Buhari ya sha yabo kan yadda ya kassara ayyukan kungiyar Boko Haram, musamman a arewa maso gabashin kasar.

Amma a watannin da suka gabata, an ga farfadowar kungiyar, inda ta rika kai hare-hare na ba-zata.

“A hakikanin gaskiya wacce ba ta da dadi, daci ne gareta, shi ne shugaban kasa ana yabonsa sallah ya zo ya kasa alwala.” In ji Dr. Usman Bugaje, tsohon dan majalisar wakilan Najeriya yayin wata hira da Umar Faruk Musa.

Ya kara da cewa “duk wadannan abin da ake fada na tsaro, da cin hanci da rashawa da tattalin arziki, mu dai ‘yan kasa babu abin da aka yi.”

Ko da yake, Bugaje, ya ce, za a iya yi wa Buhari uzuri na rashin lafiya, amma ya ce lokaci bai kure mai ba idan yana so ya yi gyara.

Daga irin ra’ayoyin jama’a da Muryar Amurka ta tattara, babu abin da ya fi ci wa mutane tuwo a kwarya a Najeriya kamar matsalar garkuwa da mutane da ta zama ruwan dare a sassan kasar.

Wani abin da wasu suka kwatanta a matsayin na takaici shi ne, yadda mutane ke biyan makudan kudade domin a saki makusantansu da aka kama, a daidai lokacin da jama’ar kasar ke fama da tsadar rayuwa.

Amma, Malam Garba Shehu, Kakaki a Fadar gwamnatin ta Najeriya ya ce, gwamnatin tarayya, ba ta gaza ba wajen ganin an tabbatar da tsaro a kasar.

“Ana nan ana karfafawa jami’an tsaro kwarin gwiwa, ana kara masu makamai ana ba su hakkinsu – wannan ma za a yi maganin wannan ma da ya taso.” Shehu ya fada a wata hira da ya yi wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa.

Dangane da batun cin hanci da rashawa kuwa, Shehu ya ce, “babbar nasar ma da ya kamata a duba ba wai ta maganar kudi da aka kakkabo su akan mutane da suka ha’inci kasa suka diba ba…. kudi ya fi biliyan dubu, wato tirilyan guda na naira,” da aka kwato.

Amma a ganin, Shehu, “babu babbar nasara da aka samu da ta wuce ta gyara hali da ake samu daga ‘yan Najeriya.”

Karar PDP Kan Sakamakon Zaben 2019

Wani batu da masu lura da al'amura suka ce zai iya zama alakakai ga shugaba Buhari shi ne, shari'ar da ake yi a kotun sauraren korafe-korafen zabe.

Jam'iyyar PDP da dan takararta Atiku Abubakar, sun shigar da kara suna kalubalantar sakamakon zaben da ya ba shugaba Buhari nasara a watan Fabarairun da ya gabata.

A cewar jam'iyyar, tuni har ta samu nasarori biyu da ke nuna alamun za ta kai ga gaci.

Da farko ta nemi shugabar kotun Justice Zainab Bulkachuwa da ta sauka daga shugabancin kotun, saboda alakar mai gidanta wanda Sanata ne yanzu haka karkashin jam'iyya mai mulki ta APC.

Nasara ta biyu kuwa ita ce, a makon da ya gabata kotun kolin kasar ta mika kujerar gwamnan jihar Zamfara ga jam'iyyar adawa ta PDP, bayan da ta ruguza dukkan kuri'un da APC ta samu a zaben jihar.

Kotun dai ta ce jam'iyyar ta APC a matakin jiha, ba ta bi ka'idojin da suka dace ba wajen gudanar da zaben fidda da gwani.

Masu lura da al'amura sun ce, akwai alamu da ke nuna cewa, sakamakon da zai fito daga wannan shari'a a kotun korafe-korafen zaben, abu ne da ba a da tabbacin yadda zai kasance.

Arewa Ta Zuba Ido Kan Wannan Wa'adi Na Biyu

Wani kalubale kuma shi ne, shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba daga arewacin kasar, inda ya fito, inda kuma a nan ne ya fi samun kuri'u, kan cewa a wa'adinsa na farko, ya fi fifita kudancin kasar da ba su ba shi kuri'u ba.

Hakan kuma ya faru ne, duk da cewa, a farkon hawansa, Buhari ya furta cewa, yankin da ya zabe shi zai fi mayar da hankali akai wajen gudanar da ayyuka, lamarin da har ya janyo suka daga kudancin Najeriya.

Yanzu dai ya rage ne a ga yadda wannan wa’adi na biyu da shugaba Buhari ya tsunduma a ciki zai kaya, yayin da a wannan mako da aka rantsar da shi, sai da aka kashe mutane a hare-haren ‘yan bindiga a arewa maso yammcin Najeriyar.