Kamala Harris Ta Kammala Ziyararta A Kasar Ghana Da Tallafin $1 Biliyan Ga Mata

Kamala Harris a kasar Ghana

Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, za ta gana da 'yan kasuwa mata na kasar Ghana a yau Laraba, don tattaunawa kan karfafa tattalin arziki da jagoranci,

Mataimakiyar Shugaban kasar Amurkan, za ta sanar da tallafin dalar Amurka biliyan 1, aikinta na karshe a kasar Ghana kafin ta wuce zuwa Tanzaniya don ci gaba da ziyarar Afirka na mako guda.

Kamar yadda ofishin mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris yace, za a ba da tallafin dalar Amurka biliyan 1 da za a yi amfani da shi wajen horon aiki, tallafawa ‘yan kasuwa mata, da kuma fadada fannin dijital.

t Kamala Harris ta isa Cape Coast

A hirar shi da Muryar Amurka, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Isah mairago jibril Abbass yace wannan tallafi zai taimakawa mata ‘yan kasuwa, ta hanyar basu jari da kafa kananan masana’antu ga mata.

Kamala Harris dai, tun shigowarta kasar Ghana ranar lahadi da ta gabata, ta gana da shugaba Akuffo-Addo, sannan suka gudanar da taron manema labarai na hadin gwuiwa a fadar shugaban kasa. Haka kuma ta gudanar da lacca ga matasa da mata a dandalin Black Stars. Haka kuma ta ziyarci sansanin jiye bayi dake birnin Cape coast.

Harris Ghana

Mataimakiyar shugaban kasar, za ta bar kasar Ghana yau Laraba zuwa Tanzaniya, inda za ta gana da shugabar kasa Samia Saluhu Hassan a birnin Dares Salaam.

A ranar Juma’a kuma za ta wuce zuwa kasar Zambia; sai ranar asabar ta wuce zuwa kasar Amurka; za ta isa Amurka a ranar Lahadi mai zuwa.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Kamala Harris a kasar Ghana