Kamaru: Gwamnati ta rufe makarantu fiye da dari da hamsin a jihar arewa

'Yan gudun hijira sun isa garin Faruwa dake jihar Arewa Mai Nisa.

Sanadiyar yawan hare-haren da 'yan ta'adan Boko Haram ke kaiwa jihar arewa gwamnatin Kamaru ta rufe makarantu fiye da dari da hamsin.

Cikin wannan makon ne gwamnatin jamhuriyar Kamaru ta fitar da sanarwar rufe wasu makarantu har da na allo fiye da dar daya da hamsin.

Gwamnati tace ta dauki matakin ne saboda karfafa tsaro a jihar gannin yadda 'yan Boko Haram ke yawan kai hari a jihar,

To saidai wasu sun zargi gwamnatin da yiwa ilimi karantsaye lamarin da suka ce ka iya mayar da ilimi baya fiye da abun da suke fuskanta yanzu.

Alhaji Muhammad Yakubu shugaban matasan kasar Kamaru kuma mai bada shawara a harkokin ilimi yayi tsokaci akan rufe makarantun. Yace gwamnati bata yin abu banza.Wai malaman makarantun gwamnati tana yi masu wani kallo. Rufe makarantun zai ba gwamnati daman bincikarsu domin su san matakan da zasu dauka,

Ya kira iyaye da su yi hakuri har gwamnati ta tabbatar babu wata barazana ga lafiyar al'umma a kaar,

Iyaye sun nuna rashin jin dadinsu kasancewa 'ya'yansu na gida zaune saboda an rufe makarantu..

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamaru: Gwamnati ta rufe makarantu fiye da dari a jihar arewa - 2' 41"