KAMARU: Malaman Makarantun Sakandire Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani

Yajin aiki a Kamaru

Malaman Makarantun Sakandare sun yi tir da jajircewar gwamnati da karya alkawuran da ta dauka yayin da su ka shiga yajin aiki dna neman biyan albashin su, bayan shekaru da yawa na jinkiri.

Malaman Makarantun Sakandaren sun hadu ne a karkashin tutar hadin gwuiwa na kungiyoyin OTS, OTA da kungiyar Malaman Makarantun Kamaru da Afirka (SECA), inda suka fara yajin aiki yau Litinin.

Zanga-zangar yajin aiki

Matsalolin malaman sakandare biyu ne. Na farko dai ya shafi "bashin da malaman suke bin gwamnati sakamakon jinkiri da aka samu wajen biyan albashi". Shekaru da dama da suka gabata ba a biya malamai albashin da aka dau alkawarin biya kai tsaye da zarar sun fara aiki ba. Hakan ya kan sanya jinkiri shekaru 5 ko ma 10, inji wasu daga cikin su.

Yajin aiki a Kamaru

Akwai kuma batun wani mataki da aka tsara kuma aka sanya hannu tun daga shekara ta 2000 wanda kawai ake jira a fara aiwatar da dokar da zai shafi kula da jin dadin rayuwar malaman.

Kungiyoyin OTS, OTA da kuma SECA sun kuma yi kira ga malaman sakandare da kada su shiga duk wani biki da ya shafi ranar malamai ta duniya, da za a gudanar ranar Laraba 5 ga wannan watan na Oktoba.

Saurari rahoton Mohamed Ladan:

Your browser doesn’t support HTML5

KAMARU: Malaman Makarantun Sakandire Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba-Ya-Gani