Sai Kamaru Ta Ga Bayan Boko Haram-inji Ministan Sadarwa

Shugaban Kamaru Paul Biya

A wani jawabi da yayi akan ta'adancin da Boko Haram ke haddasawa a kasar Kamaru ministan sadarwa Bakari ya fada cewa shugaban kasar ya dukufa kain da nain ya ga bayan kungiyar

Yace kamar yadda shugaban kasa ya bada umurni sojojin kasar suna nan suna farautar 'yan Boko Haram da nufin kawar dasu daga kasar.

Sojojin zasu cigaba da yin arangama da 'yan ta'adan har sai sun kakkabesu duka.

An debi kwanaki ana jan hankulan jama'a kan bada hadin kai wajen fallasa duk wani abu da ake shakka dashi ko kuma wani da ba'a saba dashi ba.

Tuni a birnin Marwa, birnin da ya ga bala'in 'yan Boko Haram, jama'ar garin sun sa ido sosai har sun kama wasu da bamabamai da suke shirin tarwatsawa a masallacin Juma'a. Dalili ke nan da gwamnati ke kara kira mutane su lura. Kada su yi sakaci.

Ministan ya kara da kiran jama'a musamman na arewacin kasar da kada su gaza wurin bada hadin kai da hukumomin tsaro ta hanyar basu labaran siri da zasu taimaka masu bankado 'yan ta'ada.

Da ya koma kan kafofin yada labarai sai yace su daina nuna hotunan gawarwaki da suka soma rubewa domin yin hakan bai dace ba. Ya kara da cewa kada su razana da barazanar banza da kungiyar Boko Haram ke yi masu.

Ga rahoton Manmadu Danda.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamaru Sai Ta Ga Bayan Boko Haram-inji Ministan Sadarwa