Kamaru Za Ta Dauki Mataki Akan 'Yan Aware

Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya

Shugaba Paul Biya na Kamaru, ya ce zai ragargaza dukkan ‘yan ta’addan da ya ce suna kokarin raba kasarsa biyu, ko kuma suna yin amfani da ita a zaman mabuya domin kai hari kan kasashe makwabtanta.

A cikin wani jawabin da Shugaba Biya ya yi ga kasar, ya ce hakkinsa ne ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da hadin kan kasar Kamaru. A dalilin haka, ya bayarda umurnin da a dauki dukkan matakan murkushe wadanda suka dauki makamai, suke aikatawa ko suke goyon bayan zub da jinni, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da su gaban kotu an hukumta su.

Wakilin Muryar Amurka, Moki Edwin Kidzeka, yace mutane da yawa sun sa ran shugaba Biya zai nuna sassauci ga ‘yan tawaye tare da gayyatarsu zuwa kan teburin shawarwari.

Mr. Biya yace ya umurci gwamnati da ta gudanar da tattaunawa mai ma’ana da bangaren kasar mai Magana da harshen Ingilishi domin samo hanyar biyan bukatunsu. Amma kuma ya kara da cewa zai ga bayan dukkan wadanda suka dauki makami suna yakar hukumomin kasar wadda yace zata ci gaba da kasancewa kasa daya.

Duk da haka yayi alkawarin aiwatar da tanadin tsarin mulkin kasar na kara ikon cin gashin kai ga yankunan kasar.