Kamfanin Facebook Zai Fito Da Wasu Matakan Kare Kutse Musamman a Lokacin Zabe

Kamfanin sada zumunta na Facebook yace zai fadada damammaki ga 'yan siyasa su tallata manufofi da tsare-tsaren su, yayin da a hannu guda kuma kamfanin ke daukar tsauraran matakan dakile yunkurin yin amfani da kafar sa wajen yada kalaman batanci a tsakanin 'yan siyasa.

Baya ga haka, kamfanin na Facebook na kokorin bullo da tsauraran matakai ta hanyar kimiyyar fasaha domin kare kutsen bayanai musamman a lokutan zabe a kasashe daban-daban na duniya,

A zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Daraktar kula da harkokin siyasa da cibiyoyin ketare ta kamfanin na Facebook, Katie Harbath tace yanzu haka kamfanin ya zabi Najeriya, da India, da Ukraine da kuma kasashen dake karkashin kungiyar Turai domin aiwatar da sabon tsarin.

Dr. Abbati Bako, masanin kimiyyar siyasa ne da harkokin sadarwa a fagen dimokaradiyya, yace kasar India ita ce dimokradiyya mafi girma a duniya, inda manyan ‘yan siyasa zasu iya amfani da shafin na Facebook wajen tallata manufofinsu saboda yawan masu amfani da shafin.

Shi kuwa Malam Abdulganiyu Rufa'i, kwararre akan fasahar dakile kalaman batanci ta kafar sadarwar zamani, yayi karin bayani ne dangane da sabbin matakan kamfanin Facebook. Yace a matakin Najeriya sun nuna cewa zasu yi kokari su ga sun tabbatar da cewa ba a yarda dan wata kasa ya sanya wata tallar siyasa ba sai dai ‘yan Najeriya da kansu, kuma zasu yi kokarin dakile duk wani labarin da ake hasashen ba na gaskiya bane.

Dangane da batun kutsen bayanai kuwa, akwai masu ganin cewa, mizanin ci gaban fasahar sadarwa da Najeriya keda shi bai kai a yi mata kutse ba ta hanyar kwamfuta.

Haka zalika, kwararren ya yi tsokaci kan yadda kamfanin na Facebook ka iya tsaftace tallikan 'yan siyasa kafin su kai ga abokan mu'amalar sa.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wata kotun majistire dake Kano ta yanke hukuncin zaman kaso na shekara guda babu zabin tara akan wani matashi mai suna Mustafa Jarfa, bayan tabbatar da laifin kalaman batanci ta kafar sadarwa ta Facebook ga mataimakin gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin Facbook Zai Fito Da Wasu Matakan Kare Kutse Musamman a Lokacin Zabe - 5'14"