Kananan Ma’aikata Sun Shiga Yajin Aiki A Nijar

Wadansu 'yan jamhuriyar Nihar suna jira su shiga mota a Kasuwar Katangua dake birnin Ikko

Kananan Ma'aikata a Jamhuriyar Nijar sun shiga yajin aiki da nufin ganin gwamnati ta kyautata rayuwarsu.
Kananan ma’aikata sun shiga yajin aiki na kwana biyu a jamhuriyar Nijar da zumar tursasawa gwamnati ta biya bukatunsu ta hanyar sa hannu kan wani kundin da zai kyautata rayuwar ma’aikatan da suka haura dubu shida.

Ma’aikatan sun bayyana cewa, gwamnatin Jamhuriyar Nijar bata dauki kananan ma’aikata da muhimmanci ba, ta haka bata kulawa da wahala da kuma bukatunsu, suka kuma ci alwashin ci gaba da tursasawan gwamnati har sai sun sami biyan bukata.

Babban magatakardar hadakar kungiyar kananan ma’aikatan Kamarat Gagara Tasau ya bayyana cewa, kananan ma’aikata basu cin moriyar duk wani aikin da gwamnati ke yi na kyautata rayuwar ma’aikata da ya hada da gidaje da kuma taimakon jinyar likita idan su, ko iyalansu basu da lafiya.

Wakilinmu Abdoulaye Mamman Amadou ya bayyana cewa, ma’aitan sun shiga yajin aikin ne a daidai lokacin da majalisar ministoci take zama.

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin aiki a Nijar:2:39