Kanfanoni a jihar Kaduna sun dauki matakin yaki da cutar kanjamau

Wata mata mai fama da cutar kanjamau

Kamfanonin Total tare da hadin kamfanin mai na Total PLC na Najeriya sun dauki matakin yaki da cutar kanjamau a jihar Kaduna.

Kamfanonin Total tare da hadin kamfanin mai na Total PLC na Najeriya sun dauki matakin yaki da cutar kanjamau a jihar Kaduna.

Kamfanonin sun kashe Naira miliyan 15 wajen sayen kayan aikin gwajin kwayar cutar kanjamau da kuma magunguna tare kuma da daukar nauyin bada shawarwari ga duk wanda yake bukata a jihar.

Da take Magana yayin kaddamar da shirin wayar da kan al’umma da kuma yaki da cutar kanjamau da kula da masu fama da cutar a jihar Kaduna, mataimakiyar janar manajan kamfanin, Mrs Nkoyo Attah ta bayyana cewa, kamfanin ya dauki matakin ganin yunkurin yayi tasiri ne ta wajen tada tsimin jama’a a tsakanin al’ummomin da kamfanin ke harkokin kasuwanci.

Tace kamfanin ya kuma tsaida shawarar kai shirin gwajin kwayar cutar kanjamau ga mazauna yankunan karkara tare da sayen injunan gwaji na zamani da kamfanin ya bayar gudummuwa ga asibitin Kujama dake Kaduna.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da aka sake samun bulla cutar shan inna bayan shafe shekaru biyu ba tare da samun ko yaro daya dauke da cutar ba.