Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’ar Jos ta kirkiro wata cibiyar yaki da zazzabin cizon sauro


Sauro da yake kawo ciwon zazzabi

Jami’ar Jos karkashin cibiyar fasahar amfani da kwayar halitta ta samar da tsiro mai ganye domin yakin zazzabin cizon sauro.

Jami’ar Jos karkashin cibiyar fasahar amfani da kwayar halitta ta samar da wani tsiro mai ganye da ake kira “Artemisia Annua” amfani da shi wajen maganin zazzabin cizon sauro domin shawo kan nau’in cutar da bata jin magani.

Jami’ar ta noma ta kuma girbe kilogram 283 na ganyen wanda ake amfani da shi wajen jinyar zazzabin malariya.

Shugaban Jami’ar Jos Farfesa Hayward Mufuyai ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a dakin taron jami’ar. Ya kuma bayyana cewa, an sami nasarar shirin ne sakamakon zurfin bincike da kuma kwazon masu ilimin kimiyya daga sassa dabam dabam na jami’ar da suka gudanar da bincike kan stiron “Artemisia annua” da aka noma a yankin Gangnim dake Karamar Hukumar Langtan ta jihar Plato.

Bisa ga cewar shugaban jami’ar, bincike ya nuna cewa Artemisinin, sinadarin da aka fi bukata wajen harhada maganin zazzabin cizon sauro, shine maganin da yafi kaifi wajen maganin nau’in zazzabin cizon sauro da baya jin magani.

Ya kuma bayyana cewa, masu ilimin kimiyya sun gudanar da bincike mai zurfi kan nau’in tsiron domin sanin kasar da ta dace da shuka ta a jihar Plato. Noman ganyen “Artemisia annua” da ake bukata wajen sarrafa maganin zazzabin cizon sauro mai yawa a jihar ya tabbatar da kasuwar wannan shukar mai ban al’ajibi a Najeriya inda ake fama da cutar zazzabin cizon sauro.

Farfesa Mafuyai ya kuma bayyana cewa, ana gudanar da aikin ne karkashin shirin ilimantarwa a fannin kimiyya da Fasaha na manyan makarantu matakin B, na ma’aikatar ilimi ta tayyara tare da hadin guiwar Babban bankin duniya.

Bisa ga cewarshi, jami’ar Jos ta sayi irin “Artemisia annua” daga kasar China ta fara gwadawa domin ganin ko za a iya shukawa ya kuma girma a jihar Plato, abinda ya kai ga nasarar noma shi da yawa.

Shugaban jami’ar Jos ya bayyana cewa ya dauki jami’ar shekaru hudu tana gudanar da bincike da nazari mai zurfi da kuma gwaje gwaje kafin cimma wannan nasarar da ya hakikanta zai shawo kan matsalar zazzabin cizon sauro da ake fama da shi a kasar da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya kamar yadda shugaban tawagar binciken ya bayyana.

Farfesa Mufuyai ya kuma yi kira ga kamfanonin harhada magunguna su hada hannu da jami’ar Jos dangane da wannan ci gaba da aka samu, su kuma yi aiki tare da manoman wajen samun isasshen ganyen da ake bukata. Shugaban jami’ar ya kuma shiga noman Artemisinin a cikin gida domin maganain zazzabin cizon sauro. Bisa ga cewarshi, noman Artemisinin zai bunkasa ayyukan kamfanonin harhada magunguna a Najeriya ya kuma sa maganin zazzabin cizon sauro ya yi arha, da kuma shawo kan samar da jebun magunguna da ake dangantawa da shigo da magunguna daga kasashen waje.

Dubban ‘yan Najeriya ne ke mutuwa kowacce shekara sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG