Kano: Daidaituwa Tsakanin Hukumar Kwastan da 'Yan Kasuwa

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar (Nigerian customs and excise boss, Abdullahi Dikko Inde)

An samu sulhu tsakanin hukumar kwastan ta Najeriya da wasu 'yan kasuwa a Kano wadanda hukumar ta kama kayansu saboda rashin bin ka'idoji da biyan harajin da ya kamata

.Wannan matakin da hukumar kwastan ta dauka ya jawo cecekuce tsakaninta da 'yan kasuwan.

Yayinda wasu 'yan kasuwan ke goyon bayan hukumar wasu kuma da ake zarginsu da zama 'yan barandan 'yan kasar China suna kyamar matakin suna kuma kalubalantarsa.

Amma a lokacin da yake jawabi a wurin wani babban taro da hukumar kwastan ta yi da 'yan kasuwa da shugabannin masana'antu da masaku da masu noman auduga shugaban hukumar Abdullahi Dikko Inde ya nuna cewa an dauki matakan kawo masalaha.

Inde ya kara da cewa tilas ne fa 'yan kasuwa su dauki matakan da suka kamata domin su farfado da masana'antunsu kuma a samu ayyukan yi a cikin kasa. Yace a koyaushe jami'in gwamnati yayi aiki bisa ga abun da aikin ya tanada wani lokaci akan bashi mummunar fahimma.

Hukumar kwastan bata yin doka. Aikin da tayi a Kano doka ce aka bata aka ce ta yi. Wadanda suke korafin ana cutarsu su ne masu masana'antu da suke shigo da kaya suna kuma gurbatasu. Inde yace yana da kyau su ba hukumar tasu bahasi akan yadda suke cutuwa.

Yace to sun yiwa hukumar bayani. Sun kuma gamsu. Yace abun takaici kayan daga waje ake yiwosu amma kuma sai a rubuta Najeriya da sunan kamfaninsu. Idan kuma sun yi zane na atanfar da suke son su yi sai a saci zanen a je kasar waje a yi atanfar kuma a sayar da ita kudi zube lamarin dake durkusar da masana'antunsu.

Hukumar kwastan ta basu tabbas cewa zasu yi aiki tukuru ba gudu ba ja da baya bisa ga dokokin da aka basu saboda duk wanda ya zo Najeriya yin kasuwanci dole ne ya kiyaye dokokin kasar. Duk wanda ya taka doka kuma dokar zata takashi.

Inde yace duk shagunan da suka rufe a Kano na mutanen China ne. Babu wani mutumin Kano da aka rufe shagonsa saidai 'yan barandan 'yan China din wadanda suna ganin 'yan China nada bakin yin magana su shawo kan hukumar. Su ne suke zuwa masallatai suna addu'o'i domin hukumar ta lankwashe ta ki yin abun da kasa ta ce.

Tun ranar da suka kama kayan sun ce su biya haraji a sake masu kayan. Wadanda kuma suke ganin sun biya haraji su kawo takardunsu. Masu yiwa 'yan China baranda basa son su biya haraji.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Kano: Daidaituwa Tsakanin Hukumar Kwastan da 'Yan Kasuwa - 3' 51"