Karin Mutum 404 Sun Kamu Da COVID-19 a Najeriya

Kwayar cutar coronavirus

Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya ya zarta 42,000 a ranar Laraba 29 ga watan Yuli, a cewar hukumar da ke sa ido kan cututtuka masu yaduwa wato NCDC, yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a kasar da ta fi mai yawan al’umma a nahiyar Afrika.

A bayannan da ta ke fidda wa a kowacce rana a shafinta na Twitter, hukumar NCDC ta ce an samu karin mutum 404 da suka kamu da cutar abinda ya sa gaba dayan adadin ya kai 42,208.

A cewar hukumar, cikin mutum 42,208 da suka kamu da cutar ya zuwa yanzu, 19,004 sun warke kuma an sallame su daga asibiti yayin da mutum 873 suka mutu.

Hukumar ta kuma ce an samu karin adadin ne daga jihohi 19 na kasar: Lagos-106, Birnin tarayya Abuja-54, Rivers-48, Plateau-40, Edo-29, Enugu-21, Oyo-20, Kano-18, Ondo-15, Ogun-10, Ebonyi-9, Ekiti-8, Kaduna-6, Cross River-5, Kwara-4, Anambra-3, Delta-3, Imo-2, Nasarawa-2, sai kuma Borno-1.