Karo Na Biyu Karamin Yaro Ya Mutu A Tsare Kan Iyakar Amurka

Gawar karamar yarinya da ta mutu a kan iyakar Amurka

An sake samun wani yaro dan kasar Guatemala da ya mutu yayin da yake tsare a hannun jami’an tsaron kan iyakar kasar Amurka.

Yaron dan shakaru 8 da haihuwa wanda ba a bayyana sunanasa ba, ya rasu ne a tsakiyar daren kirsimeti, ranar da aka binne daya yarinyar da ta mutu lokacin da suke tsare a hannun jami'an tsaron kan iyakar, 'yar shekaru 7, a kauyen su da yake kasar Guatemala.

Hukumar kula da kan iyakokin Amurka ta ce yayin da yaron da mahaifinsa su ke tsare ranar litinin, jami’an sun ce sunga alamun yaron ya nuna wasu alamomin rashin lafiya.

Likitoci a asibitin dake Almogordo, New Mexico, sun duba shi suka kuma gano cewa yana fama da zazzabi da mura, suka kuma rubuta masa magunguna suka sallame shi.

A ranar litinin da daddare zuciyar sa taringa tashi ya fara amai, aka maida shi asibiti, inda ya mutu a taskiyar daren. Kawo yanzu ba a iya tabbatar da dalilin mutuwarsa ba, sai dai jami'an kan iyaka sun bada tabbacin gudanar da cikakken bincike.