Kasar Nijer Na Taron Tsara Manufofin Kare Kai Daga Rigingimu

Nijer ta kasance a tsakiyar kasashe uku masu fama da tashin hankali da rashin zaman lafiya wato Najeriya da Mali da kuma Libiya

Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Koli mai neman dawwamar da zaman lafiya a Nijer ne suka shirya taron

Wasu kwararru daga yankuna daban-daban na kasar Jamahuriyar Nijer na gudanar da wani taron binciko dalilan dake haifar da fitintinu da tashe-tashen hankula tsakanin al'ummar kasar domin a samar da hanyar magance su.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron samar da hanyoyin wanzuwar zaman lafiya a kasar Nijer.- 3':11"

Hukumar raya karkara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, da Hukumar Koli mai Fafutukar Dawwamar da Zaman Lafiya a Nijer ne suka hada guiwa su na gudanar da taron da nufin tsara wani kundin da hukumomin kasar Nijer zasu yi amfani da shi su yi rigakafin afkuwar rigingimu a kasar, musamman ma idan aka yi la'akari da cewa kasar ta Nijer na zagaye da kasashen dake fama da karancin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamamne Amadou ne ya hada rahoton kuma ya aiko.