Kasar Nijar Zata Fara Saida Man-Fetur Ga Makotan Kasashe

A jamhuriyar Nijar yau shugaba Mahamadou Issoufou, ya jagoranci bukin dasa tubalin farkon soma aiyukan shimfida bututun mai daga matatar Zinder zuwa garin Torodi dake yankin Tilabery. a wani yunkurin fitarda man kasar zuwa kasuwanin yammacin Afirka. lamarin da zai bada damar samarda aikin yi ga miliyoyon matasa.

Bututun wanda za a shinfida da ya kai tsawon kilomit 1,070, wata hanya ce ta fitarda man da jamhuriyar Nijar ke tacewa a Zinder, don isar da shi kasuwanin kasashen Mali, Burkina da Faso. Lamarin da zai bada damar rage cinkoson ababen hawa, da ma takaita hatsura akan hanyoyin zirga zirga.

Dala biliyan $1 na Amurka kasar China za ta kashe domin wannan aiki da ake saran kammalawa a tsawon shekaru 2.

Shugaban kamfanin CN Pipe Line Company na cewa aikin shinfida bututun zai kunshi wasu cibiyoyin kan hanya a kalla 10, ya yinda za a yi jona domin isarda tatacen man zuwa Tahoua.

Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasar Nijar Zata Fara Saida Man-Fetur Ga Makotan Kasashe 2'20"