Kasashen Duniya Sun Tattauna Kan Libya

Mambobin kasashen da suka halarci taro kan Libya a Jamus (AP)

Ministocin harkokin waje da manyan jami’an gwamnatocin kasashe da dama, sun yi wani taro yau Lahadi a Jamus domin duba yadda za a karshen rikicin Libya.

Taron na zuwa ne, bayan da kasashen da ke da ra’ayi kan yakin basasar kasar ta Libya da aka jima ana yi, suka amince su mutunta haramcin da aka saka kan safarar makamai tare da nuna cikakken goyon baya ga matsayar tsagaita wuta da aka cimma.

An yi taron ne a gefen babban taron kasa da kasa kan tsaro na Munich, wanda ya hado har da hukumomin Jamus da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Jamus da Majalisar Ta Dinkin Duniya, na kokarin ganin sun dakile hanyoyin da bangarorin da ke yaki suke samun makamai daga waje.

A ranar 19 ga watan Janairu, Sakatare Antonio Guterres, ya nuna korafinsa kan yadda ake ta take matsayar da aka cimma ta Berlin.

Ya ce har yanzu ana ci gaba da safarar makamai zuwa cikin Libyar, lamarin da ya ce yana kara rura wutar rikicin.

Tun a shekarar 2011, Libya ta fada cikin kangin yaki bayan da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi, wanda aka kashe daga baya.