Kashi 53% Na Marasa Lafiya Suna Jinyar Kansu

Wani marasa lafiya ya zauna kan gado

Wani sabon bincike a kan yadda ake jinyar cutar zazzabin cizon sauro da sida (HIV /AIDS) a Nigeriya ya nuna cewa, kashi 53% na wadanda suka kamu da cututukan ne suke jinyar kansu
Wani sabon bincike a kan yadda ake jinyar cutar zazzabin cizon sauro da sida (HIV /AIDS) a Nigeriya Wani sabon bincike a kan yadda ake jinyar cutar zazzabin cizon sauro da sida (HIV/AIDS) a Nigeriya ya nuna cewa, kashi 53% na wadanda suka kamu da cututukan ne suke jinyar kansu, wato suna shan magani ba tare da ganin likita ba.

Binciken da wata cibiyar nazari da binciken ra’ayoyin jama’a a Najeriya da ake kira NOI tare da hadin guiwar irin wannan kungiyar ta Amurka ce ta gudanar da binciken, ta wurin yin tambayoyi da tara bayanai na tsawon makonni biyu a watan Afrilu. Binciken ya nuna cewa a kalla kashi 66% na ‘yan Nigeriya sun kamu da cutar zazzabin cizon sauro a kalla sau daya a shekara, kashi 90% suka san matsalar cutar HIV/AIDS.

Kusan mutum bakwai cikin 10 sun sami malariya ko sau daya a shekara, kamar kashi 13% suka yiwa kansu magani ta wurin itatuwan gargajiya – Agbo Dogonyaro. Wasu kashi 38% suna sayen magani daga wurin saida magani.

Bisa ga bayanan da cibiyar nazari da binciken ra’ayoyin jama ta NOI, an sami cigaba sosai a kasashen duniya a yaki da zazzabin cizon sauro, yayinda yawan mutuwa ya ragu da kashi 25% a cikin 50 na kasashen duniya 99. An sami raguwar cutar ne domin kokarin kasashen duniya da kuma kayan gwaje-gwaje da bincike.

Rahoton ya nemi kasashe masu tasowa kamar Nigeriya, su rage yawan yaran da ke mutuwa ta cutar.

Zazzabin cizon sauro yana kashe kimanin mutane 660, 000 a duniya – yawanci kananan yara kasa da shekara biyar a kasar Afrika harda Nigeriya. Kuma an gano kashi 30% na yaran suna mutuwa ne ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro, wadda kashi 11% a Nigeriya suke.