Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sinadarin Bitamin E Yana Iya Rage Kiba


Sinadarin bitamin E
Sinadarin bitamin E

Kwararru sun gano cewa mai yuwuwa ne nan gaba a iya amfani da sinadarin Bitamin E wajen maganin cututuka da yawan kiba ke sawa, da suka hada da ciwon hanta da makamantan haka.

Kwararru sun gano cewa mai yuwuwa ne nan gaba a iya amfani da sinadarin Bitamin E wajen maganin cututuka da yawan kiba ke sawa, da suka hada da ciwon hanta da makamantan haka.

Masu binciken sun gano cewa, yana yiwuwa a iya amfani da sinadarin Bitamin E wajen maganin ciwon hanta da ake kira NASH a takaice wanda idan yayi muni yake zama cutar kansa.

Ko da yake likitoci sun tabbatar da cewa, sinadarin Bitamin E yana da amfani a jiki musamman ga masu fama da cututuka da suka hada da ciwon zuciya da kansa da wadansu cututuka kamar ciwon mantuwa da makamantan haka, ba a iya sanin ainihin ta wanne fanni yake taimako ba.

Wannan bincike yana iya zama da muhimmanci a fannin aikin jinya kasancewa mutane da dama basu samun sinadarin Bitamin E da suke bukata a rana.

Bisa ga cewar kwararru, mutanen da suka yi girma suna bukatar milligram 15 na sinadarin Bitamin E a rana, wanda ake samu daga abinci kamar gyada da ganye da alkali da mai.

Kawo yanzu dai babu maganin cutar da ake kira NASH abinda ya sa ya zama ciwon da yafi sawa a sakewa mutum hanta.

Cibiyar shawo kan cututuka ta Amurka ta bayyana cewa, kimanin kashi daya cikin uku na Amurkawa suna fama da matsalar yawan kiba, yayinda akalla mutum daya cikin goma na Amurkawa yake fama da ciwon suga.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG