KASUWA A KAI MAKI DOLE: Kasuwar Baje Kolin Kayayyakin Gargajiya A Damagaram

Yayin da ake hadahadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano (Baraka Bashir)

Shirin kasuwa a kai maki dole ya kai ziyara a wata kasuwar baje kolin kayayyakin gargajiya albarkacin ranar mata ta duniya da aka yi ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2023.

A kofar gidan raya al’adu na gargajiya da ke birnin Damagaram na jamhuriyar Nijar aka kafa wannan kasuwa.

Mata daga kungiyoyi da dama ne suka baje kolin kayayyakinsu a wannan kasuwa, da suka hada da kayan abincin gargajiya, kayan rini, da sauran kayan masarufi.

Saurari cikakken shirin da Tamar Abari ta gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

KASUWA A KAI MAKI DOLE: Kasuwar Baje Kolin Kayayyakin Gargajiya A Damagaram