Kasuwannin Hannayen Jarin Duniya Sun Fara Farfadowa

  • Ibrahim Garba

Yau Laraba, kasuwannin hannayen jari na duniya sun dan fara zaburowa, yayin da masu saka jari ke jira su ji irin matakan da babban bankin Amurka zai dauka, na ganin cewa tattalin arzikin kasar ya farfado idan annobar cutar corona ta kau.

A Asiya, ma’aunin Nikkei din Tokyo ya nuna mikewar 0.1%. Zuwa can da yamma kuma ma’aunin Hang Seng na Hong Kong bai wani sauya ba sosai, a yayin da shi kuma ma’aunin Shanghai ya dan ragu da .4%.

A Sydney, S&P/ASX bai canza ba. Shi kuma ma’aunin Sensex da ke Mumbai da TSEC na Taiwan sun yi sama da .7%, sannan KOSPI na Seoul ya yi sama da .3%.

Kasuwannin Turai kam sun fara da mikewa sosai, inda ma’aunin FTSE na London ya nuna mikewar .6%, CAC-40 na Paris ya nuna mikewar .8% sannan kuma ma’aunin DAX na Frankfurt ya nuna mikewar .9%.