Kasuwannin Hannayen Jarin Duniya Sun Zabaro

Wani dakin hada-hadar kasuwannin hannayen jari

Rahotannin da ke nuna cewa ayyukan kamfanoni a nan Amurka da ma wasu kasashe sun fara farfadowa daga annobar coronavirus, ya sa kasuwannin hannayen jarin Asia sun zaburo a yau talata.

Kasuwar Nikkin index ta Tokyo ta karkare kasuwancin a yau da Kari na kashi 1.7 cikin dari. S&P/ASX ta Sidney ta cira da kashi 1.8 cikin dari. KOSPI ta Seoul ta cira da kashi 1.2 cikin dari, TSEC ta Taipe ita ta cira da kashi 1.8 cikin dari.

Hoton alkaluman kasuwannin hannayen jarin Amurka na watannin baya

A hada hadar can da yamma, Hang Seng ta Hong Kong, ta samu karuwa har na kashi 2 cikin dari ta kasar Shanghai kuma ta fadi da digo 1, Sanseng ta Mumbai kuma ta cira da kashi 1.5 cikin dari.

An sayar da gwal akan dalar Amurka dubu $1,999.50 in da ya samu kari rabin kashi cikin dari. An saida gangan danyen mai na Amurka akan dala $40.98 yayinda samfirin Brent kuma bai sauya ba inda aka sayar akan $43.29 kowace ganga.