Kawancen 'Yan Adawan Nijar Ya Zargi Gwamnati da Karta Kudin Ayyukan Tsaro

Shugaban kasar Nijar Mahammadou Issoufou

'Yan adawan jamhuriyar Nijar na zargin gwamnati da karkata wasu kudade da kasafin kudin kasar ya ware domin ayyukan tsaro amma an kashesu kan abun da bashi da alaka da tsaro

A Jamhuriyar Nijer ‘yan adawa sun zargi gwamnatin kasar da laifin zaftare bilion 5 na sefa daga kason da aka warewa ayyukan tsaro a tsarin kasafin kudade domin anfani da su a shirin kafa kamarorin bideo a fadar shugaban kasa ISUHU MAHAMADU. Tuni bangaren masu rinjaye ya sa kafa ya shure wannan zargi.

A cikin wata sanarwar da kawancen FPR ya fitar a yammacin Talata ne’yan adawa suka bayyana cewa kwaskwarimar da gwamnatin kasar ta bukaci majalisar dokoki ta yiwa tsarin kasafin 2015 a makon jiya ita ce ta basu damar gano yunkurin karkata akalar wasu kudade.Onarebul TIJANI ABDULKADRI dan majalisar dokoki daga bangaren adawa yace.

Sai dai dan majalisar dokokin kasa na bangaren rinjayayeSHAFI’U MAGARYA da na tuntuba ta waya cewa ya yi.

Kawancen na ‘yan adawa ya yi barazanar gudanar da jerin gwano hade da taron gangami a ranar Lahdin dake tafe a birnin Yamai domin nuna bacin rai akan yadda al’amuran mulki ke gudana a gwamnatin jamhuriya ta 7.

Ga karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Kawancen 'Yan Adawan Njiar Ya Zargi Gwamnati da Karkata Kudin Ayyukan Tsaro