Kenya Ta Harba Tauraron Dan'Adam

Koren karbar bayanai daga tauraron dan'adam da ake kira satellite da turanci.

'Yan kasar suna murna da sowa da kallon kaddamar tauararon da masana kimiyya a jami'ar kasar suka kera.

Kenya ta dauki mataki na farko na yin harka a sararin samaniya, bayan data kaddamar wani dan karamin tauraron dan'adam a jiya jumma, wadda aka kera jami'ar Nairobi.

'Yan kasar sun cika da munrna suna sowa lokacinda ake nunawa kai tsaye kaddmar da tauraron dan'adam na farko da aka kera a kasar daga tashar bincike a sararin samaniya wadda kasar Japan tayi.

Masana kimiyya da dalibai a jami'ar ne suka kera tauraron, kuma injiniyoyin suna alfaharin cewa da wannan mataki, kenya ta shiga sahun kasashe da suke gudanar da bincike a sararhin subahana.

Sai dai masana suna cewa da sauran aiki a gaban kasar ta wannan fanni.