Kimamin 'yan sanda dubu ashirin da biyar sun hallara birnin New York domin juyayin mutuwar takwarorin aikinsu da aka kashe

Wasu 'yan sandan birnin New York

Dubban yan sanda daga duk fadin Amirka ne suka hallara a birnin New York jiya Asabar domin juyayin mutuwar takwarorin aikinsu guda biyu da wani mutum ya yi musu kwantar bauna ya kashe su a ranar ashirin ga wannan wata na disamba, mutumin daya kashe kansa bayan ya aikata wannan mumunar aiki.

Maitaimakin shugaban Amirka Joe Biden da gwamnan New York Andrew Cuomo da kuma magajin garin New York Bill de Blasio sun iske fiye da yan sanda dubu ashirin da biyar a cocin Christ Tabernacle na birnin New York domin zaman makokin Rafael Ramos daya daga cikin yan sandan da aka kashe.
Su dai, yan sanda an harbe su a lokacinda suke zaune a cikin motarsu a unguwar Brooklyn.
Kafin dan bindiga yaje ya harbe su, sai daya harbi tsohuwar budurwarsa a birnin Baltimore dake tazarar kilomita dari uku da ashirin daga New York, kuma ya ce zai yi ramuwar gaiyar kashe bakar da yan sanda suka yi a kwanan nan a lokacinda suke kokarin kama su.
Kashe bakar fata da wani dan sanda bature yayi a unguwar saint Louis a birnin Ferguson jihar Missouri da kuma wani a birnin New York sun hadasa cece ku ce da zanga zangar kin jinin yan sanda a duk fadin Amirka.
Idan kuma ba'a mance ba tarzoma ta barke bayan da aka ce ba za'a gurfanar da dan sanda daya kashe bakar fata a birnin Ferguson jihar Missouri, da kuma kiyawar da birnin New York yayi cewa ba zai caji yan sandan da suke da hannu a mutuwar farar hula, da aikata wani laifi ba.