An Kori Karar Wasu 'Yan Jarida Biyu a Myanmar

Kotun daukaka kara a Myanmar ta yi watsi da karar da wasu ‘yan jarida masu aiki a Reuters su biyu su ka daukaka.

A yau Juma'a kotun daukaka kara a Myanmar ta yi watsi da karar da wasu ‘yan jarida masu aiki a Reuters su biyu su ka daukaka, kan hukuncin da aka zartar masu na daurin shekaru bakwai a gidan yari.

An kama su Wa Lone da Kyaw Soe Oo a watan disamba shekarar 2017, akan karya dokar Myanmar ta kiyaye sirrin gwamnati.

Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce ‘yan jaridar ba su bada wata gamsasshiyar shaidar da za ta iya wanke su ba. Da ya ke karanta hukuncin, Alkalin Babbar Kotun Aung Naing ya ce, "hukuncin ya yi daidai da laifin da suka aikata."

Mutanen sun ce kamun nasu ya biyo bayan wata gadar zare da 'yan sanda su ka shirya masu saboda kawai su dakile rahotannin da su ke bayarwa kan kashe-kashen tsirarun Musulmi na kabilar 'yan Rohingya.

Babban Editan kafar labarai ta Reuters Stephen Adler, ya fada a wani rubutaccen bayani cewa mutanen biyu "na cigaba da zama a tsare ne saboda dalili guda: dalilin ko shi ne wadanda ke mulki na yinkurin danne gaskiya."