Korea Ta Arewa Da Ta Kudu Na Shirye-shiryen Gudanar Da Taron Koli

Jami'an Korea ta Arewa da na Kudu a wata ganawa da suka yi a lokacin wasannin gasar Olympics, ciki har da 'yar uwar shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta amince ta yi wani zama da makwabciyarta ta Kudu, domin share fagen wani taron koli na hadin gwiwa da kasashen biyu za su yi.

Korea ta Arewa ta amince ta zauna da makwabciyarta Korea ta Kudu a mako mai zuwa, domin a tsara yadda za a yi wani taron koli tsakanin kasashen biyu a watan Afrilu mai zuwa.

Korea ta Kudu ce ta sanar da wannan shiri a yau Asabar.

Rahotanni sun nuna cewa, ko wanne bangare zai aika da wakilai uku-uku a ranar Alhamis, zuwa kauyen Panmunjom da ke kan iyakar kasashen biyu.

Ri Son Gwon, shi ne zai kasance jam’in da zai jagorancin tawagar Korea ta Arewa a wajen wannan tattaunawa, sannan Cho Myoung-gyon ya jagoranci tawagar Korea ta Kudu.

Taron kolin da za a yi a watan na Afrilu tsakanin shugabannin kasashen biyu, wato Moon- Jae-in da kuma Kim Jong Un na Korea ta Arewa, na zuwa ne, bayan hadin kan da kasashen biyu suka yi a karkashin tuta guda domin karawa a gasar Olympics da aka kammala a Korea ta Kudu a kwanan nan.

Har ila yau, taron na zuwa ne, gabanin wata ganawa da za a yi ta gaba-da-gaba, tsakanin shugaban Amurka, Donald Trump da kuma Kim Jong Un.

Ana sa ran za a yi zaman ne a watan Mayu, domin tattaunawa kan shirin dakile gina makamin nukiliya da Korea ta Arewan ke yi.