Korea Ta Kai Kololuwar Yaki Da Coronavirus

Yadda jami'an lafiya ke yin feshi a wata kasuwa a Korea ta Kudu domin dakile yaduwar cutar coronavirus da ta kama mutum sama da 500 a kasar

Hukumomi a Korea ta Kudu sun tsaurara matakan yaki da coronavirus zuwa mataki na kololuwa.

Shugaban kasar, Moon Jae-in, ya yi kira ga jami’an kasar da kada su yi wata-wata wajen “daukan matakan” da suka dace a kokarin da suke yi na dakile yaduwar cutar.

Firai Ministan kasar ma, ya ayyana cewa, Korea ta Kudu ta shiga wani “mummunan yanayi” yayin da ake kara samun sabbin wadanda ke kamu wa da cutar.

A jiya Asabar Firai Minista, Chung –Sye-kyun ya yi wannan jawabi ga ‘yan kasar ta kafar talbijin, inda ya kwantarwa da al’umar kasar hankali.

Ya kuma ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin an dakile bazuwar cutar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke cewa, ana samun wani sabon salon yadda cutar ke yaduwa.

“Lallai muna kallon yadda al’amura ke wakana, kuma ba wai adadin ne kadai yake karuwa ba, har da ma yadda cutar ke bazuwa ta hanyoyi daban-daban.” In ji Dr Sylvie Briand, jami’a a hukumar ta WHO.

Hukumar yaki da yaduwar cutuka a Korea ta Kudu, ta ce mutum 556 ne a yanzu ke dauke da cutar ta coronavirus a kasar.