Kotu AKe Jira Kafin a Bayyana Sakamakon Bauchi - INEC

Wani zaman kotu a jihar Adamawan Najeriya

Hukumar zabe ta INEC a jihar Bauchi ta sanar da sakamakon zagaye na biyu na sake zabe da aka gudanar a jiya Asabar a wasu rumfuna dasuke yankunan kananan hukumomi 15 a sanadiyar wasu kurakurai da suka faru da suka janyo soke zabukan.

Kamar yadda hukumar zaben ta ce, sakamakon zaben da kuma bayyana wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Bauchin sai bayan kotu ta yanke hukunci kan batun shari’ar da jam’iyar APC da kuma mai takarar kujerar Muhammed Abdullahi Abubakar suka shigar.

A bayan gabatar da sakamakon zaben ne sai kakakin hukumar zaben, Ahmed Waziri Zadawa, ya yi takaitataccen wa 'yan jarida inda ya ce, "mun karbi sakamakon zaben daga kananan hukumomi 19."

Sakamakon zaben zagaye na biyu na nuni da cewar Jam’iyar PDP ta ba da tazarar kuri’u dubu biyar wa jam’iyar APC idan aka hada jimla da kuri’un zaben farko.

Sai dai yayin da ake dakon hukuncin kotun, Air Comm. Tijjani Baba Gamawa mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya shawarci 'yan takarar biyu da su rungumi kaddara kan abin da za a sanar.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu a Ke Jira Kafin a Bayyana Sakamakon Bauchi - INEC - 2'01"