Kotu Ta Wanke Gbagbo Daga Zargin Aikata Laifukan Yaki

Alkalai a kotun manyan laifuka ta duniya da ake kira ICC a takaice, sun wanke tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo.

Wasu alkalai a kotun manyan laifuka ta duniya da ake kira ICC a takaice, sun wanke tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo daga laifukan yakin da ake zargin shi da su.

Ana zargin Gbagbo da haddasa mummunan tashin hankalin da ya faru bayan zaben shekarar 2010 da ya yi sanadiyar saukarsa daga karagar mulki.

Masu goyon bayan Gbagbo sun yi ta sowa a yau Talata a lokacin da alkali Cuno Tarfusser ya sanar da hukuncin akan tsohon shugaban mai shekaru 73 da haihuwa da kuma Charles Goude, babban hadiminsa kuma tsohon ministan matasan kasar.

Tarfusser ya ce yawancin alkalan sun bayyana cewa masu gabatar da kara sun kasa iya gabatar da kwararan hujjoji akan wadanda suke zargi.

Fiye da mutane 3,000 aka kashe a kazamin tashin hankalin da ya barke a karshen shekarar 2010 da kuma farkon shekarar 2011, a lokacin da Gbagbo ya ki ya amince da cewa Alassane Outtara ne ya lashe zaben.