Kotun Daukaka Kararrakin Zabe Ta Soke Hukumcin Kotun Jahar Nasarawa

Zaman Kotu

Kotun daukaka kararrakin zabe dake zama a Abuja ta warware sakar da kotun sauraren kararrakin zabe a jahar Nasarawa tayi, inda ta ayyana gwamna mai ci, Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jahar.

A ranar biyu ga watan Oktoba na wannan shekara ne, kotun sauraren kararrakin zabe a Lafia, fadar jahar Nasarawa ta ayyana David Ombugadu na jami'iyyar PDP a matastin wanda ya lashe zaben.

To sai dai a zamanta na yau Alhamis a Abuja, kotun daukaka karar karkashin shugabancin mai shara'a, Ezekiel Ajayi tace an samu kuskure daga yadda aka duba hujjojin da suka kai ga yanke hukuncin a kotun na baya.

Da yake tsokaci kan humumcin kotun, mai ba gwamnan Nasarawa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Mr Nawani Aboki, yace kotu ta yi gaskiya.

A nashi bayanin, Alhaji Muhammad Abubakar Sadiq, wani dan jami'iyyar PDP a jahar Nasarawa, yace zasu daukaka kara zuwa kotun Allah ya isa.

Yanzu dai hankula zasu karkata ne kan yadda zata kaya a kotun koli, na daga ita sai a barwa Allah.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Abuja Ta Warware Sakar Kotun Jahar Nasarawa