Kotun Kolin Najeriya Zata Ci Gaba Da Bitar hukuncin Zaben Jihar Zamfara

Ranar Talata 17 ga watan nan na Maris ne kotun kolin Najeriya za ta dawo don ci gaba da bitar hukuncin da kotun ta yanke tun farko wanda ya dakatar da rantsar da zababben gwamnan jihar Zamfara Shehu Muktar na jam'iyyar APC, ya kuma bada umurnin rantsar da Bello Matawallen Maradu a matsayin gwamnan jihar.

Tun farko dai wani rikicin cikin gida tsakanin jiga-jigan jam’iyyar gabanin zaben shekarar 2019 ne ya janyo shigar da karar kalubalantar zaben fidda gwanin jam’iyyar, wanda ya sa kotu ta yanke hukunci kan cewa ba a gudanar da zaben bisa ka’ida ba don haka zaben dan takarar APC da sauran ‘yan majalisa ya bi ruwa.

Jigon jam'iyyar APC a jihar Zamfara Sani Gwamna, ya ce suna fatan kotun koli za ta duba hujjojin da suka gabatar don dawo da nasarar ga APC.

A na ta bangaren, gwamnatin jihar Zamfara ta ce hankalinta a kwance yake kan bitar hukuncin da ake yi saboda dama kotun kolin ce tun farko ta yanke hukuncin da ya kawar da APC don saba ka’idar hukumar zabe, a cewar Zailani Bappah mai taimakawa gwamnan jihar kan lamuran labarai.

Zuwa yanzu dai bitar zaben jihar Zamfara ce kadai ta rage a gaban kotun kolin bayan kammala ta jihar Imo da Bayelsa.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Kolin Najeriya Zata Ci Gaba Da Bitar hukuncin Zaben Jihar Zamfara