Kotun Saudiyya Ta Zartas Da Hukuncin Kisa Dangane Da Kisan Khashoggi

Saudi Arabia

Wata Kotu a kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyar da kuma wasu su uku da aka tusa keyarsu zuwa gidan kaso dangane da kisan gillar da aka yi wa dan jaridar nan dan asalin kasar Saudiyya mai suna Jamal Khashoggi a bara.

A wata sanarwar da ya fitar, mai shari’ar ya ce an zartar da hukuncin ne akan wadanda suke da hannu a kitsa kisan da kuma wadanda suka aikata kisan.

Shalaan al Shalaan, mataimakin mai shigar da kara a kasar Saudiyya, ya ce, wadannan mutane ne da suke da hannu dumu-dumu a kisan marigayin, Allah ya jikansa".

Jamal Khashoggi

Su dai wadanda aka tusa keyarsu zuwa gidan kaso, an yi haka ne bisa kama su da laifin kin tona laifin.

An yanke hukuncin a yau Litinin, bayan da yawancin lokuta aka yi ta zaman sauraren ba'asi a cikin sirri, inda aka wanke Saul-al-Qahtani, tsohon babban hadimin yarima mai jiran gado Mohammad Bin Salman daga kisan Kashoggi.

Kashoggi, wanda yake yi wa jaridar Washington Post rubutu, mai sukar gwamnatin Saudiyya kuma, an yi mashi kisan gilla bayan haka aka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul a watan Oktoban shekarar 2018.