Kugiyar Tarayyar Turai Na Fargabar Dangantakar Ta Da Amurka

Kamfanin jaridar New York Times ya bayyana cewar, masu kutse sun shiga matattarar adana bayanan harkokin diflomasiyyar kungiyar kasashen Turai na tsawon shekaru uku, inda suka samu damar nadar bayanan sirri.

Rahoton wanda jaridar ta wallafa da yammacin jiya Talata ya ce, wani kamfanin mai yaki da satar bayanai na Area 1 ne ya gano hakan. Wanda ya bai wa gidan jaridar fiye da shafuka 1,100 na wasu bayanai da ya samo.

A cewar kamfanin jaridar, wasu daga cikin bayanan sirrin sun nuna yadda kasashen Turai ke nuna rashin gamsuwarsu da gwamnatin Shugaba Trump. Da yadda kungiyar ke dari-dari da irin halayen da Trump yake nunawa kungiyar ta Tarayyar Turai, lamarin da suka ce ya haifar da matsalar tsaro.

Har ila yau, a cikin bayanan sirrin, har da bayanai da suka nuna yadda kungiyar ta EU ke kokawar yadda za ta tunkari Rasha da China. Da kuma fargabar cewa, mai yiwuwa Iran ta ci gaba da shirinta na gina makamin nukiliya.