Kungiyar Fulani Ta Miyetti Allah Ta Koka Gameda Dokar Hana Kiwo da Gwamnatin Jihar Benue Ta Kafa

Gwamnan jihar Benue tare da shugabannin Fulani

Gobe Laraba dokar hana kiwon dabbobi a jihar Benue zata fara aiki, amma kungiyar Fulani makiyaya tace ba zata lamunta da ita ba muddin gwamnatin jihar bata ware musu wuraren kiwo ba

Kungiyar Fulani makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah, ta koka da sabuwar dokar hana yawon kiwo da dabbobi da gwamnatin jihar Benue ta ayyana.

Daga ranar daya ga watan Nuwamban nan mai zuwa, wato gobe Laraba, sabuwar dokar zata fara aiki a jihar.

Fulani makiyaya sun ce dokar ta sabawa ‘yancin walwalarsu a matsayinsu na kasancewa ‘yan Najeriya.

To amma kuma gwamnatin jihar tace ta dauki matakin ne domin shawo kan yawan rikicin dake faruwa tsakanin makiyaya da manoma a jihar.

A wani taron manema labarai da mataimakin shugaban kungiyar Makiyaya ta Najeriya wato Miyetti Allah, Alhaji Useni Boso ya kira a Minna, jihar Neja, ya ce sun yi hannun riga da dokar kuma basu yarda da ita ba. Maganin matsalar shi ne a yi makiyaya da mashaya domin dabbobi.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Miyetti Allah, Kungiyar Fulani Ta Koka da Dokar Hana Kiwo da Gwamnatin Jihar Benue Ta Kafa - 2' 56"