Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Koka Kan Matsalar Tsaro a Arewa

Gwamna Ma'azu Babangida Aliyu na jihar Niger.

Taron gwamnonin arewa da aka yi a kaduna ya koka kan tabarbarewar tsaro a arewwcin kasar.
Da yake magana bayan taron da gwamnonin suka yi a kaduna ranar litinin, gwamnan Mu'azu Babangida Aliyu na jihar Nija, yace hankalinsu ya tasho sosai domin a da suna tsammanin zuwa yanzu gwamnati ta shawo kan rikicin nan 'yan Boko Harama, amma maimakon haka al'amari sain kara runcubewa yake yi.

Saboda haka gwamnonin suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara zage dantse wajen magance wannan al'amari.

Alhaji Mu'azu Babangida Aliyu, yace sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara tallafawa gwamnatocin jihohin nan uku da aka kakabawa dokar ta baci sabili da rikicin na masu tada kayar baya.

Da ya juya kan batun fulani makiyaya, gwamna Mu'azu Aliyu, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, yace mamimakon satar da ake yi a Bankuna, yanzu mabarnatan sun koma kan masu dabbobi. Saboda haka yace nan ma akwai bukatar hukumomi su tashi haikan.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Koka Kan Matsalar Tsaro a Arewa - 3:48