Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Ta Ce An Tafka Laifukan Yaki A Libiya

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta ce tana da hujjoji da suka nuna cewa bangarorin da ke takaddama da juna a kokarin karbe ikon Tripoli, babban birnin Libya sun tafka laifukan yaki.

Wani rahoto da kungiyar ta Amnesty mai hedkwata a London ta fitar a jiya Talata, ya nuna cewa mayakan sa-kai sun kashe fararen hula da dama tare da raunata wasu, ta hanyar kai hare-hare.

Kungiyar ta ce ta tattara wadannan bayanai ne a binciken da ta gudanar a yankunan da ake tafka fada, tun bayan barkewar rikici a ranar hudu ga watan Afrilu, inda tawagarta ta ziyarci wurare 33 da aka kai hare-haren sama da na kasa, ta zanta da shaidu.