Kungiyar RSF Ta Koka Kan Yadda Ake Kama 'Yan Jarida a Nijer

Taron 'yan jarida a Nijer

Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa da kasa ta RSF ta bayyana damuwa a game da koma bayan da ake fuskanta a yanzu a jamhuriyar Nijer bayan da hukumomin kasar suka kama wasu ‘yan jarida biyu da suka bada wani labari da ya shafi badakalar nan ta kudaden makamai da aka handame a ma’aikatar tsaron kasar, sai dai gwamnatin Nijer na cewa akwai rashin fahimta a game da wannan batu.

Tsarewar da aka yi wa editan jaridar Le Courrier, Ali Soumana tsawon kwanaki biyu a ofishin ‘yan sandan PJ da kullewar da ake ci gaba da yi wa ‘yar jarida Samira Sabou sama da wata daya dukkansu saboda bada labarin da ya shafi handamar kudaden makaman wani al’amari ne da ya tayar da hankalin kungiyar Reporter sans Frontieres, domin a cewarta babban targade ne ga ‘yancin aikin ‘yan jarida. Sakataren yada labaran cibiyar ‘yan jarida ta Maison de la Presse Souleyman Brah, na mai jan hankali akan illolin kama ‘yan jarida akan aiki.

To sai dai ministan watsa labaran jamhuriyar Nijer Salissou Mahamadou Habi na ganin akwai rashin fahimtar ainahin dalilan kama wadanan ‘yan jarida.

‘Yancin aikin ‘yan jarida da ‘yancin fadin albarkacin baki na matsayin ma’unin mizanin dimokradiyya a kasa wanda kuma ke shafar daraja da kimarta a idon duniya, a saboda haka gwamnatin ta Nijer ta jaddada aniyar ci gaba da sakin ragama don ganin ‘yan jarida sun gudanar da aikinsu ba tare da wata muzgunawa ba.

A makon jiya, jaridar Le Courrier ta ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da suka wawure kudaden ma’aikatar tsaro sun fara yunkurin ramka wadannan kudade a maimakon su gurfana gaban alkali, labarin da ya karade kafafen sada zumunta kuma abinda ya sa ‘yan sanda suka tsare editan jaridar kafin daga bisani alkali ya sallame shi, yayin da a farkon makon nan Samira Sabou ta gurfana a gaban kotu inda alkali mai zargi ya bukaci a yi mata dauri na tsawon makonni 5 da biyan tarar miliyan 1 na CFA a shari’ar da ke tsakaninta da dan shugaban kasar Nijer Maman Sani Issouhou Mahamadou saboda zarginsa da hannu a badakalar kudaden makaman.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar RSF Ta Koka Kan Yadda Ake Kama 'Yan Jarida a Nijer