Kungiyar SYNACO dake Kare Hakkin Malaman Kwantiragi a jamhuriyar Niger tana Yawon Fadakarwa

'yAN MAKARANTA DAKE KOYON SANA'A

Jamhuriyar Niger na da malamai kashi biyu, akwai ‘yan kwantiragi akwai kuma ma’aikatan din-din-din sai dai ‘yan kwantiragi sune suka fi shan wahala wurin samun albashi lamarin da kungiyar SYNACO ke son daidaitawa

Sanusi Almugwanda magatakardan kungiyar SYNACO ya ce sun dauki matakin zagayawa kasar ta Niger ne domin fadakar da jama’a akan wahalar da ‘yan kwantiragi suke sha. Idan an zo korar ma’aikata da ‘yan kwantiragi ake farawa.

Amma Yau Abdu na kungiyar SYNACEB, kungiyar ‘yan kwantiragi ta jihar Damagaran ya ce babu wata kungiya dake kare hakkinsu baicin tasu da suka kafa tun shekarar 2010. Ya ja kunnen malaman kwantiragi da kada su yadda da wata kungiya daban domin zata ci da guminsu ne kawai.

Yau Abdu ya musanta zargin cewa malaman kwantiragi sun yi rauni a jarabawar da aka yi masu.

Shi ma Mahamman Sanusi na kungiyar SYNACO ya yi kira ga malaman kwantiragin da su hada kawunansu, su tashi tsaye kana su maida hankalinsu bisa aikin da su keyi.

Tamar Abari nada karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar SYNACO dake Kare Hakkin Malaman Kwantiragi a jamhuriyar Niger tana Yawon Fadakarwa - 2' 50"