Kungiyar Al-shabab Ta Dauki Alhakin Harin Birnin Mogadishu

An ci gaba da jin karar harbe-harben bindiga a babban birnin Somalia har zuwa yau Jumma’a, kwana bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hare-haren bama-bamai har biyu a daya daga cikin manyan titunan birnin Mogadishu dake da yawan cinkoson jama’a.

Jami’ai sun ce mutane akalla 20 aka kashe wasu su 40 kuma sun jikkata a hare-haren bama-baman da kuma fada tsakanin ‘yan bindiga da dakarun tsaro da aka yi.

Al-Shabab, kungiyar dake da alaka da al-Qaida, ta dauki alhakin kai harin.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta al-Shaba ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa kungiyar ce ke da iko da Otel din Maka Almukarramah. Ya kara da cewa “Dakarun gwamnatin sun yi kokarin shiga ginin har sau uku, amma muka hanasu. Har yanzu mu ke iko da Otel din.” A cewar Abdiasis Abu Musab, mai magana da yawun dakarun kungiyar al-Shabab.