Kungiyar Taliban Ta Kai Hari A Wani Sansanin Soja A Kudancin Afghanistan

‘Yan kungiyar Taliban sun kaddamar da wani hari da sanyin safiyar yau Jumma’a a kan wani babban sansanin soja dake kudancin Afghanistan, har sojoji akalla 25 suka mutu, mayakan sun kuma tafi da wasu sojoji da yawa.

Jami’an Afghanistan da majiyoyin kungiyar Taliban sun ce wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai sanye kuma da kayan soja, ciki har da ‘yan kunar bakin wake ne suka afka sansanin Shorab dake lardin Helmand, inda kuma dakarun Amurka ke zaune. Da farkon harin, wani dan kunar bakin wake ya tada nakiyoyin dake dankare a cikin motar da yake a bakin babbar kofar shiga wurin, abinda ya ba sauran maharan damar shiga sansanin da ke da tsauraran matakan tsaro.

An ci gaba da gwabza fada har zuwa azahar a yau din. Sai dai jami’an Afghanistan basu tabbatar da cewa ko jami’an tsaro ne suka kashe, tare da fatattakar maharan daga sansanin ba ko a’a, saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ya kawo tsaiko.

A wata sanarwa, Ofishin gwamnan lardin ya ce akalla mahara 9, ciki har da ‘yan kunar bakin wake 3, dakarun Afghanistan suka kashe. Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani ba akan dakarun Afghanistan da aka kashe ko suka jikkata.