Kungiyar 'Yan Shi'a Ta Cika Shika-Shikan Zama Kungiyar 'Yan-Ta'adda

Abubakar Malami

Hakkin kowace gwamnati ce a ko ina ta dauki matakan da suka dace don kare ‘yan kasarta, da dukiyoyin su. Hukuncin da kotu ta dauka na ayyana kungiyar ‘yan Shi’a, a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda abune da ya dace.

A duk lokacin da wani ko wasu ke kokarin tada zaune tsaye ko kuma suke kokarin take doka, to babu shakka gwamnati na da hurumin daukar matakan da suka dace. Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ba kawai kin bin dokokin kasa takeba, harma da hasarar rayukan ‘yan kasa dama jami’an tsaro take kawowa, don haka ta cika duk wasu shika-shikan shiga cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Hukuncin da kotu ta dauka na ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, bashi da alaka ko dangantaka da yanki ko kabilanci. Hukunci ne da yayi dai-dai da irin take-take da mabiya kungiyar keyi.

Hakan shiyasa gwamnatin tarayya garzayawa kotu don neman bahasi akan dabi’un mabiya kungiyar. Tsohon ministan Shari’a kenan kuma daya daga cikin mutane da shugaba Muhammadu Buhari ya zaba, don aiki da su a karo na biyu Abubakar Malami, a wata tattaunawa da sashen Hausa yayi da shi a safiyar yau Asabar.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar 'Yan Shi'a Ta Cika Shika-Shikan Zama Kungiyar 'Yan-Ta'adda 3'10"