Wata cibiyar tallafawa mata da matasa dake garin Bauchi mai suna “Rahama Women Development” ta dukufa wajen agaza wa mata da yara matasa domin samun abin yi.
Wasu daga cikin ayyukan da kungiyar ke koyarwa sun hada da yin man shafawa, sabulu, man gyaran gashi, da dai sauran abubuwan da ake anfani dasu cikin gida.
Malama Maryam Ilya ita ce shugabar wannan cibiyar kuma ta shaida wa wakilinmu Abdulwahab Mohammed cewa daga lokacin da kungiyar ta fara aiki kawo yanzu an yaye dalibai sama da 400.
Tace manya-manyan kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa na cikin jerin wadanda suke basu tallafi, ciki ko har da hukumar UNICEF.
Wasu daga cikin abubuwan da suka samu sun hada da kekunan dinki da yadudduka.
Ga Abdulwahab Mohammed da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
Kungiyoyi Masu Zaman Kansu A Bauchi Na ci Gaba Da Tallafawa Masu Zaman Kashe Wando 3'38